Amma ku kabila ce zaɓaɓɓiya, ƙungiyar firistocin babban Sarki, tsattsarkar al'umma, jama'ar mallakar Allah, domin ku sanar da mafifitan al'amuran wannan da ya kirawo ku daga cikin duhu, kuka shiga maɗaukakin haskensa.
Ku kuma, kamar rayayyun duwatsu, bari a gina gida mai ruhu da ku, domin ku zama tsattsarkar ƙungiyar firistoci, da nufin ku miƙa hadayu na ruhu, abin karɓa ga Allah, ta wurin Yesu Almasihu,
Duk wanda yake da rabo a tashin nan na farko, mai albarka ne, tsattsarka ne. Mutuwa ta biyu ba ta da iko a kan irin waɗannan, amma za su zama firistocin Allah da na Almasihu, su kuma yi mulki tare da shi har shekara dubu.
Kamar yadda ba a iya ƙidaya rundunan sammai ba, ba a iya kuma auna yashin teku ba, haka nan zan yawaita zuriyar bawana Dawuda da Lawiyawa, firistoci, masu yi mini hidima.”