Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 65:6 - Littafi Mai Tsarki

6 “Na riga na ƙudura hukuncinsu, shari'ar da aka yanke kuwa an rubuta ta. Ba zan ƙyale abin da suka aikata ba, amma zan sāka musu

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 “Ga shi, yana nan a rubuce a gabana cewa ba zan ƙyale ba, zan yi cikakken ramuwa; zan yi ramuwa a cinyoyinsu

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 65:6
22 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Allahnmu ya zo, ba a ɓoye yake ba, Wuta mai cinyewa na tafe a gabansa, Babban hadiri kuwa na kewaye da shi.


Zan riɓaɓɓanya sakayyar da zan yi musu saboda muguntarsu da zunubinsu, domin sun ƙazantar da ƙasata da ƙazantattun gumakansu marasa rai, abin gādona kuma sun cika shi da abubuwansu na banƙyama.”


Ya Ubangiji, ka rama wa al'umman nan har sau bakwai, Saboda tsiwace-tsiwacen da suka yi maka.


Ya Ubangiji, dukan wannan bai sa ka yi wani abu ba? Ba za ka yi kome ba, kana kuwa sa mu yi ta shan wuya, har fiye da yadda muke iya daurewa?


Allah ya ce, “Na daɗe na yi shiru, Ban amsa wa jama'ata ba. Amma yanzu lokaci ya yi da zan yi wani abu, Na yi ƙara kamar matar da take fama da zafin naƙuda.


Kun aikata waɗannan duka, ni kuwa ban ce kome ba, Saboda haka kuka zaci ni kamar ku nake. Amma yanzu zan tsauta muku, In bayyana muku al'amarin a fili.


Sai na ga matattu manya da yara, a tsaitsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Sai kuma aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne Littafin Rai. Aka kuwa yi wa matattu shari'a bisa ga abin da yake a rubuce a cikin littattafan, gwargwadon aikin da suka yi.


Sa'an nan mutane waɗanda suke tsoron Ubangiji suka yi magana da junansu, Ubangiji kuwa ya kasa kunne ya ji abin da suke cewa. A gabansa aka rubuta a littafin tarihin waɗanda suke tsoron Ubangiji, suna kuwa girmama shi.


“Taya da Sidon, da dukan Filistiya, me kuke so ku yi mini? Kuna ƙoƙari ku rama mini saboda wani abu? Idan haka ne, zan rama muku da gaggawa.


Saboda haka na kwarara musu fushina, na ƙone su da wutar hasalata, na ɗora alhakin ayyukansu a bisa kawunansu, ni Ubangiji Allah na faɗa.”


Amma waɗanda zuciyarsu ta karkata zuwa ga bin ƙazantattun abubuwa masu banƙyama, zan sāka musu gwargwadon ayyukansu, ni Ubangiji na faɗa.”


Ka san irin wahalar da nake sha, Kana riƙe da lissafin yawan hawayena. Ashe, ba a rubuce suke a littafinka ba?


“ ‘Wannan ba a jibge suke a rumbunana ba, A ƙulle kuma a taskokina?


Ubangiji ya ce wa Musa, “Rubuta wannan a littafi domin a tuna da shi, ka kuma faɗa wa Joshuwa zan shafe Amalekawa ɗungum.”


Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har ya yi tozo, har yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna, da shi za a auna muku.”


Waɗansu suka yi ciwo sabili da zunubansu, Suna ta shan wahala saboda muguntarsu.


Sai ka tuna, ya Ubangiji, da muguntar kakanninsa, Kada ka manta da zunuban mahaifiyarsa.


Amma mugaye sun shiga uku, za a sāka musu bisa ga abin da suka aikata.


Ubangiji yana zuwa ya hukunta jama'arsa a duniya saboda zunubansu. Kashe-kashen da aka yi a duniya a ɓoye, za a bayyana su, ƙasa ba za ta ƙara ɓoye waɗanda aka kashe ba.


Bisa ga ayyukansu, haka zai sāka musu hasala, a kan maƙiyansa kuwa ramawa, a kan abokan gābansa, zai rama, da kuma a kan ƙasashen da suke a bakin gāɓa.


Ku kasa kunne! Waccan babbar hayaniya cikin birni, wancan amo a Haikali, amon Ubangiji ne da yake hukunta abokan gābansa!


Ni kam, idona ba zai yafe ba, ba kuwa zan ji tausayi ba, amma zan sāka musu bisa ga ayyukansu.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ