Ishaya 65:16 - Littafi Mai Tsarki16 Dukan wanda yake so ya roƙi albarka, sai ya roƙi Allah ya sa masa albarka, Allah da yake mai aminci ne. Dukan wanda zai sha rantsuwa, sai ya rantse da sunan Allah, Allah da yake mai aminci ne. Wahalan dā za su ƙare, za a kuwa manta da su.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202016 Duk wanda zai roƙi albarka a cikin ƙasar zai yi haka da gaskiyar Allah; wanda zai yi rantsuwa a cikin ƙasar zai rantse da gaskiyar Allah. Gama za a manta da wahalolin baya a kuma ɓoye su daga idanuna. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'an nan na ga kursiyai, da waɗanda aka bai wa ikon hukunci, zaune a kai. Har wa yau, kuma na ga rayukan waɗanda aka fille wa kai saboda shaidar da suka yi wa Yesu, da kuma Maganar Allah, ba su kuwa yi wa dabbar nan da siffarta sujada ba, ba su kuma yarda a yi musu alamarta a goshinsu ko a hannunsu ba, sun sāke rayuwa, sun yi mulki tare da Almasihu har shekara dubu.