Ishaya 65:1 - Littafi Mai Tsarki1 Ubangiji ya ce, “Na shirya in amsa addu'o'in mutanena, amma ba su yi addu'a ba. Na yi shiri domin su same ni, amma ba su ko yi ƙoƙarin nemana ba. Al'ummar ba ta yi addu'a a gare ni ba, ko da yake a koyaushe ina a shirye domin in amsa cewa, ‘Ga ni nan, zan taimake ku.’ အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20201 “Na bayyana kaina ga waɗanda ba su tambaye ni ba; ina samuwa ga waɗanda ba su neme ni ba. Ga al’ummar da ba tă kira bisa sunana ba, Na ce, ‘Ga ni, ga ni.’ အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |