Ishaya 64:7 - Littafi Mai Tsarki7 Ba wanda ya juyo gare ka ya yi addu'a, ba wanda ya je gare ka neman taimako. Ka ɓuya mana, ka kuwa yashe mu saboda zunubanmu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20207 Babu wanda yake kira bisa sunanka ko ya yi ƙoƙarin riƙe ka; gama ka ɓoye fuskarka daga gare mu ka kuma sa muka lalace saboda zunubanmu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Don me mutanena ba su amsa ba Sa'ad da na je wurinsu domin in cece su? Don me ba su amsa ba sa'ad da na yi kiransu? Ba ni da isasshen ƙarfin da zan fanshe su ne? Ina da iko in sa teku ya ƙafe ta wurin umarnina, Ina kuma da iko in sa rafuffukan ruwa su zama hamada, Kifayen da suke ciki su mutu saboda rashin ruwa.