Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 64:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Za su karkaɗu kamar ruwan da yake tafasa a wuta. Ka zo ka bayyana ikonka a kan abokan gābanka, ka sa al'ummai su yi rawar jiki a gabanka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Kamar sa’ad da wuta takan ci rassa ta sa ruwa ya tafasa, ka sauko ka sanar da sunanka ga abokan gābanka ka kuma sa al’ummai su yi rawan jiki a gabanka!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 64:2
31 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji Sarki ne, Mutane suna rawar jiki, Yana zaune a bisa kursiyinsa a bisa kerubobi, Duniya ta girgiza.


Sunan wannan birni zai zama mini abin murna, da abin yabo, da darajantawa ga dukan al'umman duniya waɗanda za su ji dukan alherin da na yi dominsu, za su ji tsoro su yi rawar jiki saboda dukan alheri da dukan wadata da na tanada musu.”


Ubangiji ya ce, “Ba za ku ji tsorona ba? Ba za ku yi rawar jiki a gabana ba? Ni ne na sa yashi ya zama iyakar teku, Tabbatacciyar iyaka, wadda ba ta hayuwa, Ko da yake raƙuman ruwa za su yi hauka, ba za su iya haye ta ba, Ko da suna ruri, ba za su iya wuce ta ba.


Yanzu dai, ya Ubangiji Allahnmu, ka cece mu daga Assuriyawa domin dukan al'umman duniya su sani kai ne Allah kai kaɗai.”


Ya ce, “Ku yi shiru, ku sani ni ne Allah, Maɗaukaki ne cikin sauran al'umma, Maɗaukaki kuma a duniya!”


Zan taurare zuciyar Fir'auna, zai kuwa bi ku, ni Ubangiji zan nuna ɗaukakata a bisa Fir'auna da dukan rundunansa. Masarawa kuwa za su sani ni ne Ubangiji.” Haka kuwa Isra'ilawa suka yi.


Ina Ubangiji yake wanda ya yi manyan al'amura da ikonsa ta wurin Musa, ya raba ruwan teku a gaban jama'arsa, domin ya yi wa kansa madawwamin suna?”


Amma duk da haka ya cece su, kamar yadda ya alkawarta, Domin ya nuna ikonsa mai girma.


Ya Allahna, ka warwatsa su kamar ƙura, Ka warwatsa su kamar ciyayin da iska take hurawa.


Don me al'ummai za su tambaye mu cewa, “Ina Allahnku?” Bari mu ga ka hukunta al'ummai Saboda sun zubar da jinin bayinka!


Ka sa su ji tsoro, ya Ubangiji, Ka sa su sani su mutane ne kawai.


A wannan rana ce zan fara sa al'ummai ko'ina a duniya su razana, su ji tsoronku. Sa'ad da za su ji labarinku, za su yi rawar jiki, su damu ƙwarai.’ ”


Saboda haka, jama'ar Isra'ila, Ga abin da zan yi muku, Zan kuwa yi shi duk, Sai ku yi shirin zuwa gaban Ubangiji.”


Duwatsu za su narke a ƙarƙashinsa, Kwaruruka za su tsattsage kamar kakin zuma a gaban wuta, Kamar ruwa yana gangarowa daga tsauni.


A wannan rana ƙafafunsa za su tsaya a bisa Dutsen Zaitun wanda yake wajen gabas da Urushalima. Dutsen Zaitun zai tsage biyu daga gabas zuwa yamma, ya zama babban kwari. Sashi guda na dutsen zai janye zuwa wajen kudu. Ɗaya sashin kuma zai janye zuwa wajen arewa.


Ubangiji zai yi yaƙi kamar yadda ya yi a Dutsen Ferazim da a Kwarin Gibeyon domin ya aikata abin da ya yi nufin yi, ko da yake ayyukansa suna da ban al'ajabi. Zai gama aikinsa, wannan aiki kuwa mai ban al'ajabi ne.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ