Ishaya 62:6 - Littafi Mai Tsarki6 Ya Urushalima, na sa matsara a garukanki Ba za su taɓa yin shiru ba, dare da rana. Za su tuna wa Ubangiji da alkawaransa, Ba kuwa za su bari ya manta ba! အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20206 Na sa matsara a kan katangarki, ya Urushalima; ba za su taɓa yin shiru ba, dare da rana. Ku da kuke kira bisa sunan Ubangiji, kada ku ba kanku hutu, အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bisa ga ka'idar da tsohonsa Dawuda ya tsara, sai Sulemanu ya karkasa firistoci ƙungiya ƙungiya domin su yi hidima, Lawiyawa kuma bisa ga matsayinsu na yin yabo da hidima a gaban firistoci, kamar yadda aka wajabta kowace rana. Matsaran ƙofa kuma aka karkasa su ƙungiya ƙungiya bisa ga yawan ƙofofin, gama haka Dawuda, mutumin Allah, ya umarta.