Ishaya 61:3 - Littafi Mai Tsarki3 Domin in kawo wa masu makoki a Sihiyona Farin ciki da murna maimakon baƙin ciki, Waƙar yabo maimakon ɓacin rai. Ubangiji kansa zai lura da su, Za su ji daɗi kamar itace mai duhuwa. Kowa da kowa zai aikata abin da yake daidai, Za a yi yabon Allah saboda abin da ya yi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20203 in tanada wa waɗanda suke baƙin ciki a Sihiyona, in maido musu rawani mai kyau a maimako na toka, man murna a maimako na makoki, da kuma rigar yabo a maimako na ruhun fid da zuciya. Za a ce da su itatuwan oak na adalci, shukin Ubangiji don bayyana darajarsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |