Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 61:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Ya aike ni in yi shela, Cewa lokaci ya yi Da Ubangiji zai ceci mutanensa, Ya kuma ci nasara a kan abokan gābansu. Ya aike ni domin in ta'azantar da masu makoki,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 don in yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji da kuma ranar ɗaukan fansar Allahnmu, don in ta’azantar da dukan waɗanda suke makoki,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 61:2
34 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Albarka tā tabbata ga masu nadāma, domin za a sanyaya musu rai.


Wannan shi ne lokacin da Ubangiji zai kuɓutar da Sihiyona, ya kuma ɗauki fansa a kan abokan gābanta.


“Na ga al'amuransu, amma zan warkar da su, zan bi da su, in ta'azantar da su tare da masu makoki.


In yi shelar zamanin samun karɓuwa ga Ubangiji.”


suna hana mu yi wa al'ummai wa'azi, don kada su sami ceto. Ta haka a kullum suke cika mudun zunubansu. Amma fa fushin Allah ya aukar musu.


Sa'an nan 'yan mata za su yi rawa da farin ciki, Samari da tsofaffi za su yi murna. Zan mai da makokinsu ya zama murna, Zan ta'azantar da su, in ba su farin ciki maimakon baƙin ciki.


Ubangiji zai hallaka mutuwa har abada! Zai share hawaye daga idanun kowane mutum, ya kawar da kunyar da jama'arsa suke sha a duniya duka. Ubangiji ne da kansa ya faɗa!


Wannan rana ta Ubangiji, Allah Mai Runduna ce, Ranar ɗaukar fansa ce don ya rama wa maƙiyansa. Takobi zai ci, ya ƙoshi, Ya kuma sha jininsu, ya ƙoshi, Gama Ubangiji Allah Mai Runduna zai hallaka maƙiyansa, A arewa, a bakin Kogin Yufiretis.


Sa'ad da kuka ga wannan ya faru, za ku yi murna, wannan zai ba ku ƙarfi da lafiya. Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji, mai taimakon masu biyayya gare ni, ina kuwa nuna fushina a kan abokan gābana.”


Ubangiji ya ce wa jama'arsa, “Idan lokacin da zan cece ku ya yi, zan nuna muku alheri. Zan ji kukanku in taimake ku. Zan tsare ku in kiyaye ku, Zan kuwa yi wa dukan mutane alkawari ta wurinku. Zan bar ku ku sāke zama a ƙasarku wadda take kufai a yanzu.


Ku faɗa wa dukan wanda ya karai, ku ce, “Ka ƙarfafa, kada kuwa ka ji tsoro! Allah yana zuwa domin ya kuɓutar da kai, Yana zuwa domin ya ɗauki fansa a kan abokan gābanka.”


“Albarka tā tabbata gare ku, ku da kuke mayunwata a yanzu, domin za a ƙosar da kuke. “Albarka tā tabbata gare ku, ku da kuke kuka a yanzu domin za ku yi dariya.


Domin ya ce, “Na saurare ka a lokacin samun karɓuwa, Na kuma taimake ka a ranar ceto.” Ga shi, yanzu ne lokacin samun karɓuwa! Ga shi kuma, yau ce ranar ceto!


Domin haka fa yanzu, sai ku kasa kunne ga abin da Ubangiji Mai Runduna, Allah mai iko na Isra'ila, yake cewa, “Zan ɗauki fansa a kanku ku maƙiyana, ba za ku ƙara wahalshe ni ba.


A wannan rana, Ubangiji Mai Runduna zai ƙasƙantar da kowane mai iko, da kowane mai girmankai, da kowane mai fāriya.


Ku yi ihu saboda shan azaba, ranar Ubangiji ta yi kusa. Ranar da Mai Iko Dukka zai kawo hallaka.


Ubangiji yana fushi da al'ummai duka, da kuma dukan sojojinsu. Ya zartar musu da hukuncin hallaka.


Ubangiji ya ce, “Ka ta'azantar da jama'ata. Ka ta'azantar da su!


Irin azumin da nake so ke nan ne? Wato ranar da mutum zai ƙasƙantar da kansa kawai. Wato ku sunkuyar da kanku ne kamar jema, ku kuma shimfiɗa tsumma, ku barbaɗa toka a inda kuke zama. Kun iya ce da wannan azumi, karɓaɓɓiyar rana ga Ubangiji?


Ubangiji ya ce wa Urushalima, “Baƙi ne za su sāke gina garukanki, Sarakunansu kuma za su bauta miki. Na hukunta ki da fushina, Amma yanzu zan nuna miki alheri da jinƙai.


Amma ni ina cike da iko, Da Ruhun Ubangiji, Da shari'a da ƙarfin hali, Don in sanar wa Yakubu da laifinsa, Isra'ila kuma da zunubinsa.


Ubangiji ya ce, “Ni ne wanda yake ƙarfafa ku. Don me za ku ji tsoron mutum mai mutuwa, Wanda bai fi ciyawa tsawon rai ba?


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ