Ishaya 60:9 - Littafi Mai Tsarki9 Jiragen ruwa ne suke zuwa daga manisantan ƙasashe, Suna kawo mutanen Allah gida. Suna tafe da azurfa da zinariya, Domin su girmama sunan Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Wanda ya sa dukan al'ummai su girmama mutanensa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20209 Babu shakka tsibirai suna dogara gare ni; jiragen Tarshish kuma su ne a gaba, suna kawo ’ya’yanki maza daga nesa, tare da azurfa da zinariya, domin su girmama Ubangiji Allahnki, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, gama ya cika ki da daraja. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |