Ishaya 60:6 - Littafi Mai Tsarki6 Babban ayarin raƙuma zai zo daga Madayana da Efa. Za su zo daga Sheba, su kawo zinariya da kayan ƙanshi. Mutane za su ba da labari mai daɗi a kan abin da Allah ya yi! အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20206 Manyan ayarin raƙuma za su cika ƙasar, ƙananan raƙuma ke nan daga Midiyan da Efa. Daga Sheba kuma duka za su zo, suna ɗauke da zinariya da turare suna shelar yabon Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Wannan shi ne jawabin da Allah ya yi a kan dabbobin da suke kudancin hamada, “Jakadu sun yi tafiya a ƙasa mai hatsari, inda zakoki suke, inda macizai masu dafi da macizai masu tashi sama suke. Suna labta wa jakunansu da raƙumansu kayayyaki masu tsada da za su kai gaisuwa ga al'ummar da ba za ta taimake su da kome ba.
Sa'ad da Sarauniyar Sheba ta ji labarin irin suna da Sulemanu ya yi, sai ta zo Urushalima don ta jarraba shi da tambayoyi masu wuya. Ta zo da 'yan rakiya masu yawa, da raƙuma ɗauke da kayan yaji, da zinariya mai yawa, da duwatsu masu daraja. Sa'ad da ta zo wurin Sulemanu, ta faɗa masa dukan abin da yake a ranta.