Ishaya 60:18 - Littafi Mai Tsarki18 Ba za a ƙara jin hayaniyar tashin hankali ba, Ba za a ƙara aukar wa ƙasar da ɓarna ba. Zan kiyaye ki, in kāre ki kamar garu, Za ki yi yabona domin na cece ki. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202018 Ba za a ƙara jin hayaniyar tashin hankali a ƙasarki ba, balle lalacewa ko hallaka a cikin iyakokinki, amma za ki kira katangarki Ceto ƙofofinki kuma Yabo. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Zan nuna wa jama'ata Isra'ila wuri na kansu inda zan kafa su su zauna. Ba wanda zai sāke damunsu. Mugayen mutane kuma ba za su ƙara wahalshe su kamar dā ba, tun lokacin da na naɗa wa jama'ata Isra'ila mahukunta. Zan hutar da kai daga fitinar abokan gābanka duka. Banda wannan kuma ina shaida maka, cewa, zan sa gidanka ya kahu.