Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 6:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Saboda haka sai ya ce mini in tafi in faɗa wa jama'a wannan jawabi cewa, “Kome yawan kasa kunne da za ku yi, ba za ku fahimta ba. Kome yawan dubawar da za ku yi, ba za ku san abin da yake faruwa ba.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Ya ce, “Je ka ka faɗa wa wannan mutane, “ ‘Kome yawan kasa kunne da za ku yi, ba za ku fahimta ba; Kome yawan dubar da za ku yi, ba za ku san abin da yake faruwa ba.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 6:9
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai ya ce, “Ku kam, an yarda muku ku san asiran Mulkin Allah. Amma ga sauran sai da misali, don gani kam, su gani, amma ba za su gane ba. Ji kuma, su ji, amma ba za su fahimta ba.


don gani da ido kam, su gani, amma ba da zuci ba. Ji kuma, su ji, amma ba za su fahimta ba, wai don kada su juyo a yafe musu.”


“Ya makantar da su, ya kuma taurarar da zuciya tasu, Kada su gani da idanunsu, su kuma gane a zuci, Har su juyo gare ni in warkar da su.”


Yadda yake a rubuce cewa, “Allah ya toshe musu basira, Ya ba su ido, ba na gani ba, Da kuma kunne, ba na ji ba, Har ya zuwa yau.”


Ubangiji ya ce, “Waɗannan mutane sun ce suna mini sujada, amma kalmominsu ba su da ma'ana, zukatansu kuma suna wani wuri dabam. Addininsu ba wani abu ba ne, sai dai dokoki ne da ka'idodin mutane da suka haddace.


Allah ya ce, “Kirawo mutanena a ɗakin shari'a. Suna da idanu, amma makafi ne, Suna da kunnuwa, amma kurame ne!


Ubangiji kuma ya ce masa, “Ka raɗa masa suna, Ba-mutanena-ba-ne, gama ku ba mutanena ba ne, ni kuma ba Allahnku ba ne.


Duk da haka har wa yau Ubangiji bai ba ku zuciyar ganewa, ko idanun gani, ko kunnuwan ji ba.


Mugaye ba su san gaskiya ba, amma waɗanda suke yi wa Ubangiji sujada sun san ta sosai.


Ubangiji ya sa ku ku yi gyangyaɗi ku yi barci mai nauyi. Annabawa ne ya kamata su zama idon jama'a, amma Allah ya rufe idanunsu.


Don haka zan firgita su ba zato ba tsammani, da dūka a kai a kai. Waɗanda suke da hikima za su zama wawaye, dukan wayon nan nasu kuwa ba zai amfana musu kome ba.”


‘Ku ji wannan, ya ku wawaye, marasa hankali, Kuna da idanu, amma ba ku gani, Kuna da kunnuwa, amma ba ku ji.’ ”


“Ɗan mutum, kana zaune a tsakiyar gidan 'yan tawaye da suke da idanun gani, amma ba sa gani, suna da kunnuwa na ji, amma ba sa ji, gama su 'yan tawaye ne.


Saboda haka ne Ubangiji zai koya muku baƙaƙe baƙaƙe, da shaɗara shaɗara, da babi babi. Sa'an nan kowane ɗaga ƙafar da kuka yi, za ku yi tuntuɓe, za a yi muku rauni, a kama ku a tarko, a kai ku kurkuku.


Isra'ila, kun ga abu da yawa, Amma bai zama da ma'ana a gare ku ba ko kaɗan. Kuna da kunnuwan da za ku ji, Amma a ainihi me kuka ji?”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ