Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 6:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Ko da mutum ɗaya cikin goma zai ragu a ƙasar, shi ma za a hallaka shi. Zai zama kamar kututturen itacen oak wanda aka sare.” Wato kututturen alama ce ta tohuwar jama'ar Allah zuwa gaba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Ko da yake kashi ɗaya bisa goma zai ragu a ƙasar, za tă sāke zama kango. Amma kamar yadda katambiri da itacen oak sukan bar kututturai sa’ad da aka yanke su, haka iri mai tsarkin nan zai zama kututture a ƙasar mai tsarki.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 6:13
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

ta wurin zuriyarka kuma al'umman duniya za su sami albarka, saboda ka yi biyayya da umarnina.”


Gama sun auro wa kansu da 'ya'yansu 'yan matan mutanen nan. Yanzu tsattsarkar zuriya ta cuɗanya da mutanen ƙasashe. Shugabanni da magabata sun fi kowa laifi kan wannan rashin gaskiya.”


Da ba don Ubangiji ya taƙaita kwanakin nan ba, da ba ɗan adam ɗin da zai tsira. Amma sabili da zaɓaɓɓun nan da ya zaɓa, sai ya taƙaita kwanakin.


Ashe, ba kai da ita Allah ya maishe ku jiki ɗaya da ruhu ɗaya ba? Me Allah yake nufi da wannan? Yana so 'ya'yanmu su zama 'yan halal masu tsoron Allah. Domin haka ku kula fa, kada kowa ya ci amanar matarsa ta ƙuruciya.


Da a ce Ubangiji Mai Runduna bai rage sauran jama'a ba, da an hallakar da Urushalima gaba ɗaya, kamar yadda aka yi wa Saduma da Gwamrata.


Kakannin kakannin nan kuma nasu ne, Almasihu kuma, ta wurin zamansa mutum, na kabilarsu ne. Yabo yā tabbata ga Allah har abada, shi da yake bisa kome. Amin.


Duk wanda aka rage a Urushalima, wanda Ubangiji ya nufa da rayuwa, za a ce da shi mai tsarki.


Ba don an taƙaita kwanakin nan ba, da ba ɗan adam ɗin da zai tsira. Amma sabili da zaɓaɓɓun nan za a taƙaita kwanakin.


Gama ku jama'a ce tsattsarka ta Ubangiji Allahnku. Ubangiji Allahnku ya zaɓe ku daga cikin dukan al'ummai don ku zama jama'arsa, abar mulkinsa.


Gidan sarautar Dawuda kamar itacen da aka sare ne, amma kamar yadda rassa sukan toho daga cikin kututture, haka nan za a sami sabon sarki daga zuriyar Dawuda.


“‘Duk da haka zan bar waɗansunku da rai, gama waɗansu daga cikinku za su tsere wa takobi, amma zan watsa su cikin sauran al'umma.


Ubangiji ya ce, “Wani birnin Isra'ila ya aika da soja dubu, Ɗari ne kaɗai suka komo, Wani birni kuma ya aika da soja ɗari ne, Amma goma kaɗai suka komo.”


Ni Ubangiji na ce sulusi biyu na ƙasar za su hallaka, Sulusi ɗaya ne kawai zai ragu.


Ko da yake kuna da yawa kamar taurarin sama, za ku zama 'yan kaɗan, domin ba ku yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku ba.


Amma a yanzu a wannan ɗan lokaci Ubangiji Allahnmu ya yi mana alheri da ya bar mana ringi, ya kuma ba mu wuri a wurinsa mai tsarki, inda za mu zauna lafiya domin Allahnmu ya waye mana ido, ya kuma ba mu 'yar wartsakewa daga bautarmu.


Za su mallaki ƙasar Assuriya da takobi, Su shiga ƙofofin ƙasar Nimrod da zararren takobi, Zai cece mu daga hannun Ba'assuriye, Sa'ad da ya kawo wa ƙasarmu yaƙi, Sa'ad da kuma ya tattake ƙasarmu.


Zan kuwa bar mutane masu tawali'u, Da masu ladabi a cikinka, Su kuwa za su nemi mafaka a wurin Ubangiji.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ