Da jin motsin mahayan dawakai da na maharba Kowane gari zai fashe. Waɗansu za su shiga kurama, Waɗansu kuma su hau kan duwatsu. Dukan birane za su fashe tas, Ba wanda zai zauna a cikinsu.
“Ubangiji zai warwatsa ku cikin dukan al'ummai daga wannan bangon duniya zuwa wancan. Can za ku bauta wa gumakan itace da na dutse waɗanda ku da kakanninku ba ku san su ba.
Sai Nebuzaradan shugaban sojojin, ya kwashe sauran mutanen da suka ragu a birnin, da waɗanda suka gudu zuwa wurin Sarkin Babila, da sauran da suka ragu, ya kwashe ya kai su zaman talala.
Zan shafe mutum da dabba, Zan shafe tsuntsayen sararin sama da kifayen teku, Zan kuma rushe gumakansu tare da mugaye, Zan kuma datse ɗan adam daga duniya.