Ishaya 57:6 - Littafi Mai Tsarki6 Rabonku yana cikin duwatsu masu sulɓi na cikin kwari. A gare su kuka kwarara hadaya ta sha, kuka kawo hadaya ta gari. Kuna tsammani zan ji daɗin waɗannan al'amura? အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20206 Gumakan da suke cikin duwatsu masu sulɓi su ne rabonku; su ɗin, su ne rabonku. I, gare su kuka kwarara hadayu na sha kuka kuma miƙa hadayu na gari. Saboda waɗannan abubuwa, zan yi haƙuri? အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Mutane suna yin abin da suka ga dama. Suna kashe bijimi domin hadaya, ko su yi hadaya da mutum. Sukan yi hadaya da ɗan rago, ko kuwa su karye wuyan kare. Sukan miƙa hadaya ta hatsi, ko kuwa su miƙa jinin alade. Suna miƙa turare, ko kuwa su yi addu'a ga gumaka. Suna jin daɗin al'amuran banƙyama a lokacin yin sujada.