21 Allah ya ce, “Ba salama ga mugaye.”
21 “Babu salama ga mugaye,” in ji Allahna.
Ubangiji ya ce, “Ba mafaka domin masu zunubi.”
Hanyar salama ba ku san ta ba. Ba adalci a hanyoyinku, kukan karkatar da hanyoyinku, ba wanda zai yi tafiya lafiya a cikinku.
Amma mugaye sun shiga uku, za a sāka musu bisa ga abin da suka aikata.
Da Yehoram ya ga Yehu, sai ya ce, “Lafiya dai?” Yehu ya ce, “Ina fa lafiya, tun da karuwanci da sihirin uwarka, Yezebel, sun yi yawa haka?”
Na ce, “Na yi aiki, amma a banza ne. Na mori ƙarfina, amma ban ƙulla kome ba.” Duk da haka na dogara ga Ubangiji, ya daidaita al'amura, Shi zai sāka mini abin da na yi.
Wato annabawan Isra'ila waɗanda suka yi annabci a kan Urushalima, suka ga wahayin salama dominta, ga shi kuwa, ba salama, ni Ubangiji Allah na faɗa.”