Ishaya 57:13 - Littafi Mai Tsarki13 Sa'ad da kuka ta da murya kuka yi kuka, to, bari tattaruwar gumakanku su cece ku! Iska za ta fauce su, numfashi zai kawar da su. Amma wanda ya fake gare ni zai mallaki ƙasar. Zai kuma yi sujada a Haikalina.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202013 Sa’ad da kuka nemi taimako, bari tarin gumakanku su cece ku! Iska za tă kwashe dukansu tă tafi, ɗan numfashi kawai zai hura su. Amma mutumin da ya mai da ni mafakarsa zai gāji ƙasar ya kuma mallaki dutsena mai tsarki.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |