Ashe, abin gadon nan nawa ya zama dabbare-dabbaren tsuntsun nan ne mai cin nama? Tsuntsaye masu cin nama sun kewaye shi? Tafi, ka tattaro namomin jeji, Ka kawo su su ci.
“Ni Ubangiji Allah na ce, kai ɗan mutum, sai ka gayyato kowane irin tsuntsu da dukan bisashe daga ko'ina, su zo idi wanda nake shirya musu a duwatsun Isra'ila. Za su ci nama su kuma sha jini.
Zan yashe ka, kai da dukan kifayen kogunanka cikin jeji. Za ka fāɗi a fili, ba kuwa wanda zai ɗauke ka, ya binne ka. Zan sa ka zama abincin namomin jeji da tsuntsayen sararin sama.