Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 56:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Haka Ubangiji Allah, shi wanda ya tattara Isra'ilawa korarru, ya faɗa, ya ce, “Zan ƙara tattaro waɗansu, bayan waɗanda na riga na tattara.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Ubangiji Mai Iko Duka ya furta cewa, zai tattara korarru na Isra’ila, “Zan ƙara tattaro waɗansu bayan waɗanda na riga na tattara.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 56:8
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ina kuma da waɗansu tumaki da ba na wannan garke ba ne. Su ma lalle in kawo su, za su kuwa saurari muryata, su zama garke guda, makiyayi kuma guda.


“A ɗan ƙanƙanen lokaci na rabu da ke, Amma da ƙauna mai zurfi zan sāke karɓarki.


Duk wannan kuwa shiri ne, domin a cikar lokaci a harhaɗa dukkan abubuwa ta wurin Almasihu, wato abubuwan da suke sama, da abubuwan da suke a ƙasa.


“Ku ji maganar Ubangiji, Ya ku al'ummai, Ku yi shelarsa har a ƙasashen da suke nesa, na gāɓar teku. Ku ce, ‘Shi wanda ya warwatsa Isra'ila zai tattaro ta, Zai kiyaye ta kamar yadda makiyayi yakan kiyaye garkensa.’


Yana riƙe da sandan mulkinsa, Ya sa shi a tsakanin ƙafafunsa, Har Shilo ya zo. Zai mallaki dukan jama'o'i.


ba ma saboda jama'a kaɗai ba, har ma yă tattaro 'ya'yan Allah da suke warwatse ko'ina su zama ɗaya.


Ubangiji ya ce, “A waccan rana zan tattara guragu, Da waɗanda aka kora, Da waɗanda na wahalshe su.


Mutanen Yahuza da mutanen Isra'ila za su haɗu su zama ɗaya, Za su zaɓa wa kansu shugaba ɗaya. Za su shugabanci ƙasar Gama ranar Yezreyel babba ce.”


Zan mayar muku da lafiyarku, Zan kuma warkar da raunukanku, Ko da yake maƙiyanku suna kiranku yasassu, Suna cewa, ‘Ai, Sihiyona ce, ba wanda ya kula da ita.’ Ni Ubangiji na faɗa.”


Ubangiji Allah ya ce wa jama'arsa, “Zan nuna alama ga al'ummai, Za su kuwa kawo 'ya'yanku gida.


Mutanena za su zo daga can nesa, Daga Birnin Sin a kudu, Daga yamma, da arewa.”


Zan faɗa wa kudu su bar su su tafi, Arewa kuma kada su riƙe su a can. Bari mutanena su komo daga manisantan ƙasashe, Daga kowane sashi na duniya.


Ubangiji yana rayar da Urushalima, Yana komo da waɗanda aka kai su baƙunci a wata ƙasa.


Ka cece mu, ya Ubangiji Allahnmu, Ka komo da mu daga cikin sauran al'umma, Domin mu yabi sunanka mai tsarki, Mu kuma yi murna mu yi maka godiya.


Sai Yahudawa suka ce wa juna, “Ina za shi da har ba za mu same shi ba? Za shi wurin Yahudawan da suka warwatsu a cikin al'ummai ne, ya koya wa al'umman?


Kamar yadda makiyayi yakan nemo tumakin da suka watse daga cikin garkensa, haka zan nemi tumakina. Zan cece su daga dukan wuraren da aka watsar da su a ranar gizagizai da baƙin duhu.


Ubangiji ya ce mini, “Bawana, ina da aiki mai girma dominka, Ba komo da girman jama'ar Isra'ila da suka ragu kaɗai ba, Amma zan sa ka zama haske ga al'ummai, Domin dukan duniya ta tsira.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ