Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa, ko ɗan'uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji’ ba, gama su duka za su san ni, tun daga ƙarami har zuwa babba. Zan gafarta musu laifofinsu, ba kuwa zan ƙara tunawa da zunubansu ba.”
Wannan shi ne alkawarin da zan yi da jama'ar Isra'ila, Bayan kwanakin nan, in ji Ubangiji, Wato, zan sa shari'una a birnin zuciyarsu, In kuma rubuta su a allon zuciyarsu. Zan kasance Allahnsu, Su kuma su kasance jama'ata.
Allah mai kawo sa zuciya, yă cika ku da matuƙar farin ciki da salama saboda bangaskiyarku, domin ku yi matuƙar sa zuciya ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.
Ku kam, shafar nan da kuka samu daga Ruhu Mai Tsarki tā tabbata a zuciyarku, ba sai wani ya koya muku ba. Amma kamar yadda shafar nan tasa take koya muku kome, ita kuwa gaskiya ce ba ƙarya ba, yadda dai ta koya muku, to, sai ku zauna a cikinsa.
“Da ma kun kasa kunne ga umarnina kurum! Da sai albarka ta yi ta kwararowa dominku Kamar ƙoramar da ba ta taɓa ƙafewa ba! Da kuma nasara ta samu a gare ku kamar raƙuman ruwa Da suke bugowa zuwa gāɓa.
“Za ku fita daga cikin Babila da murna, Za a bi da ku, ku fita daga birnin da salama. Duwatsu da tuddai za su ɓarke da waƙa, Itatuwa za su yi ta sowa don murna!
Jama'arsu za su ce, “Bari mu haura zuwa tudun Ubangiji, Zuwa ga Haikalin Allah na Isra'ila. Za mu koyi abin da yake so mu yi, Za mu yi tafiya a hanyar da ya zaɓa. Koyarwar Ubangiji daga Urushalima take zuwa, Daga Sihiyona yake magana da jama'arsa.”
“A waccan rana zan yi alkawari Da namomin jeji, da tsuntsaye, Da abubuwa masu rarrafe saboda Isra'ila. Zan kuma kakkarya baka da takobi, In kuma sa yaƙi ya ƙare a ƙasar, Sa'an nan za su yi zamansu lami lafiya.
Suna gunaguni a kaina suna cewa, “Su wa wannan mutum yake tsammani yana koya musu? Wa yake bukatar jawabinsa? Sai ga 'yan yaran da aka yaye kaɗai yake da amfani!
Ubangiji ya ce, “Zan kawo muku wadata madawwamiya, dukiyar al'ummai za ta malalo zuwa gare ku kamar kogi wanda ba ya ƙafewa. Za ku zama kamar yaro wanda mahaifiyarsa take renonsa, tana rungume da shi da ƙauna.
Al'umman duniya za su zo, su ce, “Bari mu haura zuwa tudun Ubangiji, Zuwa Haikalin Allah na Isra'ila, Za mu koyi abin da yake so mu yi, Za mu yi tafiya a hanyar da ya zaɓa.” Koyarwar Ubangiji daga Urushalima take zuwa, Daga Sihiyona yake magana da jama'arsa.
Sa'an nan mutanen Ifraimu za su zama kamar ƙarfafan jarumawa, Za su yi farin ciki kamar sun sha ruwan inabi, 'Ya'yansu za su gani su yi murna, Zukatansu za su yi murna da Ubangiji.