Ishaya 54:11 - Littafi Mai Tsarki11 Ubangiji ya ce, “Ya Urushalima, mai shan wahala, birnin da yake cikin halin ƙaƙa naka yi, Ba ki da wanda zai ta'azantar da ke. Zan sake gina harsashinki da duwatsu masu daraja. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202011 “Ya ke birni mai shan azaba, wadda hadari ya bulale ki ba a kuma ta’azantar da ke ba, zan gina ke da duwatsu turkuwoyis, zan kafa harsashenki da duwatsun saffaya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A halin yanzu dai na riga na yi iyakacin ƙoƙarina, har na tanada waɗannan abubuwa saboda Haikalin Allahna, wato zinariya saboda kayayyakin zinariya, azurfa saboda kayayyakin azurfa, tagulla saboda kayayyakin tagulla, baƙin ƙarfe saboda kayayyakin baƙin ƙarfe, itace kuwa saboda kayayyakin itace, da duwatsu da yawa masu daraja, da masu launi iri iri.