Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 53:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Amma aka yi masa rauni saboda zunubanmu, Aka daddoke shi saboda muguntar da muka aikata. Hukuncin da ya sha ya 'yantar da mu, Dūkan da aka yi ta yi masa, ya sa muka warke.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Amma aka yi masa rauni saboda laifofinmu, aka ƙuje shi saboda kurakuranmu; hukuncin da ya kawo mana salama ya kasance a kansa, kuma ta wurin mikinsa ya sa muka warke.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 53:5
27 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Domin Almasihu ma ya mutu sau ɗaya tak ba ƙari, domin kawar da zunubanmu, mai adalci saboda marasa adalci, domin ya kai mu ga Allah. An kashe shi a jiki, amma an rayar da shi a ruhu.


kamar yadda Ɗan Mutum ma ya zo ba domin a bauta masa ba sai dai domin shi ya yi bautar, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”


Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi zunubi saboda mu, domin mu mu sami adalcin Allah ta wurinsa.


Gama ta hadaya guda kawai ya kammala waɗanda aka tsarkake har abada.


wanda aka bayar a kashe saboda laifofinmu, aka kuma tashe shi, domin mu sami kuɓuta ga Allah.


Ta nufin nan ne aka tsarkake mu, ta wurin miƙa jikin Yesu Almasihu hadaya sau ɗaya tak, ba ƙari.


Jawabi mafi muhimmanci da na sanar da ku, shi ne wanda na karɓo, cewa, Almasihu ya mutu domin zunubanmu, kamar yadda Littattafai suka faɗa,


shi Almasihu ma, da aka miƙa shi hadaya sau ɗaya tak, domin ya ɗauke zunuban mutane da yawa, zai sāke bayyana, bayyana ta biyu, ba a kan maganar kawar da zunubi ba, sai dai domin yă ceci waɗanda suke ɗokin zuwansa.


Ku yi zaman ƙauna kamar yadda Almasihu ya ƙaunace mu, ya kuma ba da kansa dominmu, sadaka mai ƙanshi, hadaya kuma ga Allah.


“An ƙayyade wa jama'arka da tsattsarkan birninka shekara ɗari huɗu da tasa'in domin a kawo ƙarshen laifi da zunubi, domin a yi kafarar laifi, sa'an nan a shigo da adalci madawwami, a rufe wahayi da annabci, a tsarkake Haikali.


Zan sa ƙiyayya tsakaninka da matar, tsakanin zuriyarka da zuriyarta, shi zai ƙuje kanka, kai za ka ƙuje diddigensa.”


“Ka farka, ya kai takobi, ka fāɗa wa makiyayina, Ka fāɗa wa mutumin da yake kusa da ni, Ka sari makiyayin domin tumakin su watse. Zan bugi ƙanana da hannuna, Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.


Ko da yake shi Ɗa ne, ya koyi biyayya ta wurin wuyar da ya sha,


Yau fa ku sani ba da 'ya'yanku nake magana ba, waɗanda ba su sani ba, ba su kuma ga hukuncin Ubangiji Allahnku ba, da girmansa, da ƙarfin ikon dantsensa,


Na roƙi taimako a gare ka, ya Ubangiji Allahna, Ka kuwa warƙar da ni.


Wani lokaci sai mun sha wuya muke sāke hanyoyinmu.


Ya taɓa leɓunana da garwashin wutar ya ce, “Wannan ya taɓa leɓunanka, yanzu fa an kawar da laifofinka, an kuma gafarta maka zunubanka.”


Ka ƙarfafa jama'ar Urushalima. Ka faɗa musu sun sha wahala, ta isa, Yanzu kuwa an gafarta musu zunubansu. Na yi musu cikakken hukunci saboda dukan zunubansu.”


“Na ga al'amuransu, amma zan warkar da su, zan bi da su, in ta'azantar da su tare da masu makoki.


Mala'ikan da zai yi masa alheri ya ce, ‘Ka cece shi daga gangarawa zuwa cikin kabari, Na sami abin da zai fanshe shi!’


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ