Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 52:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Ubangiji ya nuna ikonsa mai tsarki, Ya ceci jama'arsa, Dukan duniya kuwa ta gani.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Ubangiji zai nuna hannunsa mai tsarki a fili a idanun dukan al’ummai, da kuma dukan iyakokin duniya za su gani ceton Allahnmu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 52:10
27 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya Ubangiji, ka tashi, ka taimake mu! Ka nuna ikonka, ka cece mu, Ka nuna ikonka kamar yadda ka yi a dā. Kai ne ka daddatse dodon ruwa, wato Rahab.


Dukkan 'yan adam kuma za su ga ceton Allah.”


Sa'an nan na ga wani mala'ika yana kaɗawa a tsakiyar sararin sama, yana tafe da madawwamiyar bishara, domin ya sanar da ita ga mazaunan duniya, wato, ga kowace al'umma, da kabila, da harshe, da jama'a.


Ubangiji ya ce mini, “Bawana, ina da aiki mai girma dominka, Ba komo da girman jama'ar Isra'ila da suka ragu kaɗai ba, Amma zan sa ka zama haske ga al'ummai, Domin dukan duniya ta tsira.”


Wane ne ba zai ji tsoronka ba, ya Ubangiji, Ya kuma ɗaukaka sunanka? Domin kai kaɗai ne Mai Tsarki. Dukkan al'ummai za su zo su yi maka sujada, Don ayyukanka na adalci sun bayyana.”


Domin haka ubangiji ya umarce mu, ya ce, “ ‘Na sa ka haske ga al'ummai, Don ka zama sanadin ceto, har ya zuwa iyakar duniya.’ ”


Dukan al'ummai za su tuna da Ubangiji, Za su zo gare shi daga ko'ina a duniya, Dukan kabilai za su yi masa sujada.


Domin dukan duniya ta san nufinka, Dukan sauran al'umma kuma su san cetonka.


A kan Sihiyona, dutse tsattsarka, Ba wani macuci ko mugu. Ƙasar za ta cika da sanin Ubangiji Kamar yadda tekuna suke cike da ruwa.


Sa'ad da wannan ya faru, kowa zai ce, “Shi Allahnmu ne! Mun dogara gare shi, ya kuwa cece mu. Shi ne Ubangiji. Mun dogara gare shi, yanzu kuwa muna da farin ciki domin ya cece mu!”


Sa'an nan za a bayyana ɗaukakar Ubangiji, Dukan 'yan adam kuwa za su gan ta. Ubangiji ne kansa ya yi wannan alkawari.”


“Ku juyo wurina a cece ku, Ku mutane ko'ina a duniya! Ni kaɗai ne Allah da yake akwai.


Ku fita daga Babila, ku tafi a sake! Ku yi sowar albishir da farin ciki, ku sa a sani a ko'ina, “Ubangiji ya fanshi bawansa Isra'ila!”


Ya ga ba wani mutum, ba kuwa wanda zai taimaki waɗanda ake zalunta. Sa'an nan da ikon kansa ya yi nasara, adalcinsa ya goyi bayansa.


Zan yi magana domin in ƙarfafa Urushalima, Ba zan yi shiru ba, Sai na ga adalcinta ya bayyana kamar haske, Cetonta kuma ya haskaka kamar fitila da dare.


Na yi mamaki sa'ad da na duba, sai na ga ba wanda zai taimake ni. Amma fushina ya sa na sami ƙarfi, har ni kaina na ci nasara.


Shi kuwa zai tashi ya ciyar da garkensa da ƙarfin Ubangiji, Da ɗaukakar sunan Ubangiji Allahnsa. Za su kuwa zauna lafiya, Gama zai zama mai girma cikin duniya duka.


domin dukan mutanen duniya su sani Ubangiji yana da iko, domin kuma ku kasance da tsoron Ubangiji Allahnku har abada.”


Kana da ƙarfi kamar na Allah? Kana iya tsawa da murya kamar tasa?


Ubangiji zai bar kowane mutum ya ji maɗaukakiyar muryarsa, ya kuma ji ƙarfin fushinsa. Za a ga harsunan wuta, gizagizai za su ɓarke, za a yi ƙanƙara, da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.


Bari kowa da yake kusa da na nesa ya ji abin da na yi, ya kuma san ikona.”


Wane ne zai gaskata abin da muka ji yanzu? Wane ne zai iya ganin ikon Ubangiji cikin wannan?


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ