Ishaya 51:13 - Littafi Mai Tsarki13 Kuna mantawa da Ubangiji wanda ya halicce ku, Wanda ya shimfiɗa sammai, Ya kuma kafa harsashin ginin duniya? Don me za ku yi ta jin tsoron fushin waɗanda suke zaluntarku, Da waɗanda suke shiri su hallaka ku? Fushinsu ba zai taɓa yi muku kome ba! အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202013 har da kuka manta da Ubangiji Mahaliccinku, wanda ya shimfiɗa sammai ya kuma kafa harsashen duniya, har kuna zama da tsoro kowace rana saboda fushin masu zalunci, waɗanda sun ƙudura sai sun hallaka? Gama ina fushin mai zalunci? အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Yanzu, idan kuna so, sa'ad da kuka ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai ku fāɗi ƙasa, ku yi sujada ga gunkin zinariya da na kafa. Idan kun yi haka, da kyau. Amma idan ba ku yi sujadar ba, nan take za a jefa ku a tanderun gagarumar wuta, in ga ko wane ne allahn nan da zai kuɓutar da ku daga hannuna?”