Ishaya 51:11 - Littafi Mai Tsarki11 Su waɗanda ka fansa Za su kai Urushalima da farin ciki, Da waƙa, da sowa ta murna. Za su yi ta murna har abada, Ba sauran baƙin ciki ko ɓacin zuciya har abada. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202011 Waɗanda Ubangiji ya fansar za su dawo. Za su shiga Sihiyona da waƙoƙi; madawwamin farin ciki zai rufe kansu da rawani. Murna da farin ciki zai cika su, baƙin ciki da nishi zai ɓace. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
za a sāke jin muryar murna da ta farin ciki, da muryar ango da ta amarya, da muryoyin mawaƙa, sa'ad da suke kawo hadayun godiya a cikin Haikalin Ubangiji, suna cewa, “ ‘Ku yi godiya ga Ubangiji Mai Runduna, Gama Ubangiji nagari ne, Gama madawwamiyar ƙaunarsa tabbatacciya ce.’ “Gama zan mayar da arzikin ƙasar kamar yadda yake a dā, ni Ubangiji na faɗa.”