3 Ina da iko in sa sararin sama ya yi duhu, In sa ya zama makoki domin matattu.”
3 Na suturar da sararin sama da duhu na kuma mai da tsummoki abin rufuwarsa.”
Da ya ɓamɓare hatimi na shida, na duba, sai kuwa aka yi wata babbar rawar ƙasa, rana ta koma baƙa kamar gwado na gashi, gudan wata ya zama kamar jini,
Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka sama, domin a yi duhu cikin ƙasar Masar, irin duhun da za a iya taɓawa.”
To, tun daga tsakar rana, duhu ya rufe ƙasa duka, har zuwa ƙarfe uku na yamma.
Kowane tauraro, da kowace ƙungiyar taurari za su daina ba da haske. Rana za ta yi duhu lokacin da ta fito, wata kuwa ba zai ba da haske ba.
“Duniya za ta yi makoki saboda wannan, Sammai za su duhunta, Gama ni na faɗa, haka kuwa na nufa in yi, Ba zan ji tausayi ba, Ba zan kuwa fāsa ba.”
ko su zura wa ƙasa ido, amma ba abin da za su gani, sai wahala da duhu mai banrazana, inda za a kora su a ciki.