Ishaya 5:30 - Littafi Mai Tsarki30 Sa'ad da ranar ta yi, za su yi ruri a kan Isra'ila da ƙarfi kamar rurin teku. Ku duba ƙasan nan! Duhu da damuwa! Duhu ya haɗiye hasken. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202030 A wannan rana za su yi ta ruri a kansa kamar rurin teku. Kuma in wani ya dubi ƙasar, zai ga duhu da damuwa; haske ma zai zama duhu ta wurin gizagizai. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Wannan shi ne jawabin da Allah ya yi a kan dabbobin da suke kudancin hamada, “Jakadu sun yi tafiya a ƙasa mai hatsari, inda zakoki suke, inda macizai masu dafi da macizai masu tashi sama suke. Suna labta wa jakunansu da raƙumansu kayayyaki masu tsada da za su kai gaisuwa ga al'ummar da ba za ta taimake su da kome ba.