Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 5:29 - Littafi Mai Tsarki

29 Sojojinsu na ruri kamar zakunan da suka kashe nama, suna kuwa ɗauke da shi don kada wani ya ƙwace musu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

29 Rurinsu ya yi kamar na zaki, suna ruri kamar ’yan zakoki; suna yin gurnani yayinda suke kamun abin da suke farauta su ɗauke shi ba mai ƙwace shi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 5:29
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ku ji kukan makiyaya, Gama an ɓata musu darajarsu. Ji rurin zakoki, Gama an lalatar da jejin Urdun.


Ringin Yakubu kuma zai zamar wa al'umman duniya, Kamar yadda zaki yake a tsakanin namomin jeji, Kamar kuma yadda zaki yake a tsakanin garkunan tumaki, Wanda, sa'ad da ya ratsa, yakan tattaka, Ya yi kacakaca da su, Ba wanda zai cece su.


Amma yanzu an washe mutanensa, Aka kukkulle su a kurkuku, Aka ɓoye su a rami. Aka yi musu fashi, aka washe su, Ba wanda ya zo domin ya kuɓutar da su.


Shugabanninsa zakoki ne masu ruri, Alƙalansa kuma kyarketai ne da sukan fito da maraice, Waɗanda ba su rage kome kafin wayewar gari.


Zaki ya yi ruri! Wa ba zai ji tsoro ba? Sa'ad da Ubangiji ya yi magana! Wa zai ƙi yin shelar maganarsa?


“Za su bi Ubangiji, Zai yi ruri kamar zaki, hakika zai yi ruri 'Ya'yansa za su zo da rawar jiki da yamma.


Mutanen Babila za su yi ruri kamar zakuna, Su yi gurnani kamar 'ya'yan zaki.


“Isra'ilawa kamar tumaki ne waɗanda zakuna suka bi su suna kora. Da farko dai Sarkin Assuriya ne ya cinye su. Yanzu kuwa Sarkin Babila, wato Nebukadnezzar, shi ne yake gaigayi ƙasusuwansu.


Kamar yadda zaki yakan fito daga cikin kurmin Urdun, garin ya fāda wa babban garken tumaki, haka zan sa nan da nan su gudu daga gare ta. Zan naɗa wani wanda na zaɓa, gama wa yake kama da ni? Wa zai yi ƙarata? Ina makiyayin da ya isa ya yi gāba da ni?


Zaki ya hauro daga cikin ruƙuƙinsa, Mai hallaka al'ummai ya kama hanya, Ya fito daga wurin zamansa don ya mai da ƙasarku kufai, Ya lalatar da biranenku, su zama kango, ba kowa.


Ubangiji ya ce mini, “Kamar dai makiyaya ba za su iya tsoratar da zakin da ya kashe dabba ba, kome irin tsawa da ihun da suka yi, haka ni ma, ba abin da zai iya hana ni, ni Ubangiji Mai Runduna, in kiyaye Dutsen Sihiyona.


Na aiki Assuriya ta faɗa wa al'ummar da ba ta tsoron Allah, da yaƙi, wato jama'ar da ta sa na yi fushi. Na aike su su yi waso su yi sata, su tattake jama'a kamar ƙura a tituna.”


“Ku ji wannan ku da kuke ƙyale ni, In ba haka ba zan hallaka ku, Ba wanda zai cece ku.


Al'ummar tana kama da ƙaƙƙarfan zaki Sa'ad da yake barci, ba wanda zai yi ƙarfin hali ya tashe shi. Duk wanda ya sa muku albarka zai sami albarka, Duk wanda ya sa muku la'ana zai sami la'ana.”


Yahuza ɗan zaki ne, Ya kashe ganima sa'an nan ya komo wurin ɓuyarsa. Yahuza kamar zaki yake, Yakan kwanta a miƙe, Ba mai ƙarfin halin da zai tsokane shi.


Ba za a sami zakoki a can ba, Mugayen namomin jeji ba za su bi ta can ba. Waɗancan da Ubangiji ya fansar Su za su zo gida ta wannan hanya.


Nan ne inda shawararsu za ta kai ki, Waɗannan masanan taurari da kika yi ta neman shawararsu dukan kwanakin ranki. Dukansu za su bar ki, kowa ya tafi inda ya nufa, Ba wanda zai ragu da zai cece ki.”


Ina kogon nan na zakoki, Inda aka ciyar da 'ya'yan zaki, Inda zaki da zakanya da kwiyakwiyansu sukan tafi, Su tsere daga fitina?


Zakuna suna ruri a kansa, Suna ruri da babbar murya. Sun lalatar da ƙasarsa, Garuruwansa sun lalace, Ba wanda yake zaune cikinsu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ