Ishaya 5:25 - Littafi Mai Tsarki25 Ubangiji yana fushi da jama'arsa, ya miƙa hannunsa domin ya hukunta su. Duwatsu za su jijjigu, gawawwaki kuwa za a bar su a kan tituna kamar shara. Duk da haka Ubangiji ba zai huce daga fushinsa ba, ba kuwa zai janye hannunsa daga yin hukunci ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202025 Saboda haka fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kan mutanensa; ya ɗaga hannunsa ya kuma buge su. Duwatsu sun jijjigu, gawawwaki kuwa suka zama kamar juji a tituna. Saboda wannan duka, fushinsa bai huce ba, bai kuwa janye hannunsa ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Don haka Ubangiji ba zai bar ko ɗaya daga cikin samarin ya tsira ba, ba zai nuna jinƙai ga gwauraye ba, wato matan da mazansu suka mutu, ko ga marayu, gama dukan mutane maƙiyan Allah ne, mugaye, duk abin da suke faɗa mugunta ce. Duk da haka fushin Ubangiji ba zai huce ba, amma har yanzu dantsensa yana a miƙe don ya yi hukunci.