'Yan'uwa, ga wata asirtacciyar gaskiya da nake so ku sani, domin kada ku zaci ku masu hikima ne, taurarewar nan–wadda ba mai tabbata ba ce–ta sami Isra'ilawa ne, har adadin al'ummai masu ɗungumawa zuwa ga Allah ya cika.
“Kin amince da kanki cikin muguntarki, Kina tsammani ba wanda yake ganinki. Hikimarki da saninki suka sa kika ɓata, Kika kuwa ce da kanki, ‘Ni ce Allah, Ba mai kama da ni!’
Sarkin Assuriya ya yi kurari ya ce, “Dukan waɗannan ni da kaina na yi su. Ni ƙaƙƙarfa ne, mai hikima, mai wayo. Na kawar da kan iyakokin da suke tsakanin ƙasashen sauran al'umma, na kwashe dukan abin da suka tattara suka adana. Kamar bijimi, haka na tattake mutanen da suke zaune a can.