Ishaya 5:2 - Littafi Mai Tsarki2 Ya kauce ƙasar ya tsintsince duwatsun, Ya daddasa itatuwan inabi mafi kyau. Ya gina hasumiya don a yi tsaronsu, Ya kuma haƙa rami inda za a matse 'ya'yan inabin. Ya yi ta jira don 'ya'yan inabin su nuna, Amma ko wannensu tsami take gare shi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20202 Ya haƙa ƙasa ya kuma tsintsince duwatsun ya shuka mata inabi mafi kyau. Ya gina hasumiyar tsaro a cikinta ya kuma shirya wurin matsin ruwan inabi. Sa’an nan ya sa rai ga samun girbi mai kyau na inabin, amma sai ga shi inabin ya ba da munanan ’ya’ya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Isra'ila ita ce gonar inabin Ubangiji Mai Runduna, Jama'ar Yahuza su ne itatuwan inabin da aka daddasa. Ya sa zuciya za su yi abin da yake mai kyau, Amma a maimakon haka sai suka zama masu kisankai! Ya zaci za su aikata abin da yake daidai, Amma waɗanda suka fāɗa hannunsu kururuwa suke, suna neman adalci!
Zan nuna wa jama'ata Isra'ila wuri na kansu inda zan kafa su su zauna. Ba wanda zai sāke damunsu. Mugayen mutane kuma ba za su ƙara wahalshe su kamar dā ba, tun lokacin da na naɗa wa jama'ata Isra'ila mahukunta. Zan hutar da kai daga fitinar abokan gābanka duka. Banda wannan kuma ina shaida maka, cewa, zan sa gidanka ya kahu.