Amma cikin annabawa na Urushalima, Na ga abin banƙyama. Suna yin zina, suna ƙarya, Suna ƙarfafa hannuwan masu aikata mugunta, Saboda haka ba wanda ya juya ga barin muguntarsa, Dukansu suna kama da Saduma, Mazaunanta kuwa kamar Gwamrata.”
“Kun karya zuciyar adali ta wurin ƙaryarku, ko da yake ni ban karya zuciyarsa ba. Kun ƙarfafa wa mugu gwiwa, don kada ya bar hanyarsa ta mugunta, ya tsira.
Gama ƙasar cike take da mazinata, Saboda la'ana, ƙasar za ta yi makoki, Wuraren kiwo na jeji sun bushe, Manufarsu mugunta ce, Ba su mori ƙarfinsu a inda ya kamata ba.
“A lokacin nan, Zan bincike Urushalima da fitilu, Zan kuwa hukunta marasa kulawa Waɗanda suke zaman annashuwa, Waɗanda suke cewa a zukatansu, ‘Ubangiji ba zai yi alheri ba, Ba kuma zai yi mugunta ba!’
Kuna fāriya a kan alkawarin da kuka yi da mutuwa, kun ƙulla yarjejeniya da lahira. Kun tabbata masifa za ta ƙetare ku sa'ad da ta zo, domin kun dogara ga ƙarairayi da ruɗi don su kiyaye ku.