Ishaya 49:26 - Littafi Mai Tsarki26 Zan sa masu zaluntarku su karkashe juna, Za su yi māye, da kisankai, da fushi. Sa'an nan dukan 'yan adam za su sani, ni ne Ubangiji, Wanda ya cece ku, ya fanshe ku. Za su sani ni ne Allah Mai Iko Dukka na Isra'ila.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202026 Zan sa masu zaluntarki su ci naman jikinsu; za su bugu da jininsu, sai ka ce sun sha ruwan inabi. Sa’an nan dukan mutane za su sani cewa ni, Ubangiji, ni ne Mai Cetonki, Mai Fansarki, Maɗaukakin nan na Yaƙub.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Mai Fansa, Ya ce wa wanda aka raina ƙwarai, Al'ummai suka ƙi shi, Bawa na masu mulki kuma, “Sarakuna za su gan ka a sake, Su kuma miƙe tsaye su ba ka girma, Shugabanni su kuma za su gani, Su rusuna har ƙasa su ba ka girma.” Wannan kuwa zai faru saboda Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya zaɓi bawansa, Ya kuwa cika alkawaransa.