Ishaya 49:23 - Littafi Mai Tsarki23 Sarakuna za su zama kamar iyaye a gare ku, Sarauniyoyi za su yi renonku kamar uwaye. Za su rusuna har ƙasa su ba ku girma, Da tawali'u za su nuna muku bangirma. Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji, Dukan mai jiran taimakon Ubangiji, ransa ba zai ɓaci ba.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202023 Sarakuna za su zama kamar iyayen reno, sarauniyoyinsu kuma za su yi renonku kamar uwaye. Za su rusuna a gabanki da fuskokinsu har ƙasa; za su lashe ƙura a ƙafafunki. Sa’an nan za ki san cewa ni ne Ubangiji; waɗanda suke sa zuciya gare ni ba za su sha kunya ba.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Mai Fansa, Ya ce wa wanda aka raina ƙwarai, Al'ummai suka ƙi shi, Bawa na masu mulki kuma, “Sarakuna za su gan ka a sake, Su kuma miƙe tsaye su ba ka girma, Shugabanni su kuma za su gani, Su rusuna har ƙasa su ba ka girma.” Wannan kuwa zai faru saboda Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya zaɓi bawansa, Ya kuwa cika alkawaransa.