Ku raira, ku sammai! Ki yi sowar murna, ke duniya! Bari duwatsu su ɓarke da waƙa! Ubangiji zai ta'azantar da mutanensa, Zai ji juyayin mutanensa da suke shan wahala.
Saboda haka Ubangiji ya amsa ya ce, “Mace za ta iya mantawa da jaririnta, Ta kuma ƙi ƙaunar ɗan da ta haifa? Ya yiwu mace ta manta da ɗanta, To, ni ba zan taɓa mantawa da ku ba.
“Kai ɗan mutum, sai ka faɗa wa mutanen Isra'ila, ‘Kuna cewa, “Laifofinmu da zunubanmu suna nawaita mana, muna kuwa lalacewa, yanzu fa, ta ƙaƙa za mu rayu?” ’
Ubangiji ya bayyana gare ni tun daga nesa cewa, “Ya Isra'ila, budurwa! Na kusace ki da madawwamiyar ƙaunata, Ba zan fasa amintacciyar ƙaunata a gare ki ba. Zan sāke gina ki, Za ki kuwa ginu, Za ki ɗauki kayan kaɗe-kaɗe, Za ki shiga rawar masu murna.