Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 48:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Na sani kuna nuna ku masu taurinkai ne, Kuna ƙage kamar ƙarfe, kun taurare kamar tagulla.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Gama na san yadda kuke da taurinkai; jijiyoyin wuyanku ƙarafa ne, goshinku tagulla ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 48:4
27 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Ku kangararru, masu ɓatan basira, masu kunnen ƙashi, kullum kuna yi wa Ruhu Mai Tsarki tsayayya. Yadda kakanninku suka yi, haka ku ma kuke yi.


Ya kuma ce wa Musa, “Na ga jama'an nan suna da taurinkai.


Wanda ake ta tsauta wa a kai a kai, amma ya taurare, ba makawa tasa ta ƙare farat ɗaya.


Amma ga shi, saboda ƙeƙasasshiyar zuciyarka marar tuba, kana nema wa kanka fushin Allah a ranar fushi, sa'ad da za a bayyana hukuncin Allah macancani.


“Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya ce, ‘Ga shi, ina aukar wa wannan birni da dukan garuruwansa dukan masifu da na ambata a kansa, domin sun taurare zukatansu, sun ƙi jin maganata.’ ”


Ya Ubangiji, ashe, ba masu gaskiya kake so ba? Ka buge su, amma ba su yi nishi ba, Ka hore su, amma sun ƙi horuwa, Fuskarsu ta ƙeƙashe fiye da dutse, Sun ƙi tuba.


gama na san tayarwarku da taurinkanku. Tun ma ina da rai ke nan tare da ku kuka tayar wa Ubangiji, balle bayan rasuwata.


Gama Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa Isra'ilawa, ‘Ku mutane ne masu taurin kai. In na yi tafiya tare da ku, nan da nan zan hallaka ku. Domin haka fa, yanzu, ku tuɓe kayan adonku, domin in san abin da zan yi da ku’ ”


Kada su zama kamar kakanninsu, Jama'ar 'yan tawaye marasa biyayya. Ba su taɓa dogara ga Ubangiji da zuciya ɗaya ba, Ba su kuwa yi masa aminci ba.


Na dai faɗa musu su daina yanga, Su daina yin taƙama.”


Ka kama hanya zuwa ƙasa mai yalwar abinci, amma fa ba zan tafi tare da ku ba, gama ku mutane ne masu taurin kai, domin kada in hallaka ku a hanya.”


“Ku kasa kunne gare ni, ku mutane masu taurinkai, Ku da kuke tsammani nasara tana can da nisa.


Ya kuwa tayar wa sarki Nebukadnezzar wanda ya rantsar da shi da Allah. Amma ya ƙi kula, ya taurare zuciyarsa gāba da Ubangiji, Allah na Isra'ila.


Sai dai kowace rana ku ƙarfafa wa juna zuciya muddin akwai “Yau”, don kada kowannenku ya taurare, ta yaudarar zunubi.


Amma sa'ad da ya kumbura, ya taurare ransa yana ta yin girmankai, sai aka kore shi daga gadon sarautarsa, aka raba shi kuma da darajarsa.


Duk da haka ba su saurare ni ba, ba su kula su ji ba, sai suka taurare zukatansu suka aikata mugun abu fiye da na kakanninsu.


Saboda haka aka ƙi yin ruwa, Ruwan bazara bai samu ba. Goshinki irin na karuwa ne, ba ki jin kunya.


Kada ku yi taurin kai kamar yadda kakanninku suka yi, amma ku miƙa kanku ga Ubangiji, ku zo Wuri Mai Tsarki, wanda ya tsarkake har abada, ku bauta wa Ubangiji Allahnku, domin ya huce daga zafin fushin da yake yi da ku.


Duk da haka suka ƙi kasa kunne, suka taurare zuciyarsu kamar yadda kakanninsu suka yi, waɗanda ba su yi imani da Ubangiji Allahnsu ba.


Saboda haka sai ku kame zukatanku, kada ku ƙara yin taurinkai.


Sa'ad da zaman salama ya komo, sai kuma su yi zunubi, Kai kuma sai ka bar abokan gabansu su ci su. Duk da haka idan sun tuba, suka roƙe ka ka cece su, Kakan ji daga Sama, sau da yawa, Ka cece su da jinƙanka mai yawa.


Su mutane ne marasa kunya, masu taurinkai. Ga shi kuwa, na aike ka gare su, ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya faɗa.’


Sai Fir'auna ya aika, ya tambaya, ashe, ko dabba guda daga cikin na Isra'ilawa ba ta mutu ba? Duk da haka zuciyar Fir'auna ta taurare, bai kuwa saki jama'ar ba.


A kullum suna tayar wa Allah, a kullum ƙarya suke yi, a kullum suna ƙin kasa kunne ga koyarwar Allah.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ