Ishaya 48:17 - Littafi Mai Tsarki17 Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Ubangiji, wanda ya fanshe ku, ya ce, “Ni ne Ubangiji Allahnku, Wanda yake so ya koya muku domin amfanin kanku, Ya kuwa nuna muku hanyar da za ku bi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202017 Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansarku, Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya ce, “Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya koya muku abin da ya fi muku kyau, wanda ya muku hanyar da za ku bi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Mai Fansa, Ya ce wa wanda aka raina ƙwarai, Al'ummai suka ƙi shi, Bawa na masu mulki kuma, “Sarakuna za su gan ka a sake, Su kuma miƙe tsaye su ba ka girma, Shugabanni su kuma za su gani, Su rusuna har ƙasa su ba ka girma.” Wannan kuwa zai faru saboda Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya zaɓi bawansa, Ya kuwa cika alkawaransa.