Ishaya 48:14 - Littafi Mai Tsarki14 “Ku tattaru, ku duka, ku kasa kunne! Ba ko ɗaya cikin alloli da zai iya yin annabci ba, Cewa mutumin da na zaɓa, shi zai iya fāɗa wa Babila, Zai yi abin da na umarce shi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202014 “Ku tattaru, dukanku ku kuma saurara, Wanne a cikin gumakan ya iya faɗa waɗannan abubuwa? Zaɓaɓɓen da Ubangiji yake ƙauna zai aikata nufinsa a kan Babilon; hannunsa zai yi gāba da Babiloniyawa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ni kaina na iza Sairus ya yi wani abu, Don ya cika nufina ya daidaita al'amura. Zan miƙar da kowace hanyar da zai yi tafiya a kai. Zai sāke gina birnina, wato Urushalima, Ya kuma 'yantar da mutanena da suke bautar talala. Ba wanda ya yi ijara da shi, ko ya ba shi rashawa don ya yi wannan.” Ubangiji Mai Runduna ne ya faɗi wannan.