Ishaya 48:1 - Littafi Mai Tsarki1 Ku kasa kunne, ya jama'ar Isra'ila, Ku da kuke zuriyar Yahuza. Kuna rantsuwa da sunan Ubangiji, Kuna nuna kamar kuna sujada ga Allah na Isra'ila, Amma abin da kuke faɗa ba haka kuke nufi ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20201 “Ku kasa kunne ga wannan, ya gidan Yaƙub, waɗanda ake kira da sunan Isra’ila suka kuma fito daga zuriyar Yahuda, ku da kuke yin rantsuwa da sunan Ubangiji kuna kuma kira sunan Allah na Isra’ila, amma ba da gaskiya ko adalci ba, အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Zan zo wurinku domin in yi shari'a. Nan da nan zan tabbatar da laifin masu yin sihiri, da na mazinata, da na masu shaidar zur, da na masu zaluntar ma'aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu, da baƙi, da waɗanda ba su ganin girmana.”