Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 47:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Amma ba da jimawa ba, a rana ɗaya Dukan waɗannan al'amura za su faru. Kome sihirin da za ki yi, Za ki rasa 'ya'yanki, ki kuwa zama gwauruwa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Duk waɗannan za su sha kanki cikin farat ɗaya, a rana guda, rashin ’ya’ya da gwauranci. Za su zo a kanki da cikakken minzani, duk da yawan masu dubanki da kuma dukan sihirinki.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 47:9
26 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Lokacin da mutane suke cewa, “Muna zaman salama da zaman lafiya,” wuf; sai halaka ta auko musu, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba kuwa hanyar tsira.


Cikin ƙyaftawar ido aka hallaka su, Suka yi mummunan ƙarshe!


Ya faru saboda yawan karuwancin Nineba kyakkyawa mai daɗin baki, Wadda ta ɓad da al'umman duniya da karuwancinta, Ta kuma ɓad da mutane da daɗin bakinta.


Waɗanda aka hana shiga birnin kuwa, su ne fajirai, da masu sihiri, da fasikai, da masu kisankai, da masu bautar gumaka, da kuma duk wanda yake son ƙarya, yake kuma yinta.


Amma matsorata, da marasa riƙon amana, da masu aikin ƙyama, da masu kisankai, da fasikai, da masu sihiri, da masu bautar gumaka, da kuma duk maƙaryata, duk rabonsu tafkin nan ne mai cin wuta da kibiritu, wanda yake shi ne mutuwa ta biyu.”


Sai sarki ya yi kira da babbar murya, cewa a kawo masu dabo, da bokaye, da masu duba. Sai sarki ya ce wa masu hikima na Babila, “Dukan wanda ya karanta wannan rubutu, ya faɗa mini ma'anarsa, to, za a sa masa rigar shunayya, a kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa, zai zama shi ne na uku a cikin masu mulkin ƙasar.”


Sai masu sihiri, da masu dabo, da Kaldiyawa, da masu duba suka zo, na faɗa musu mafarkin, amma ba su iya yi mini fassararsa ba.


Sai sarki ya umarta a kirawo masa masu sihiri, da masu dabo, da bokaye, da Kaldiyawa, su zo su fassara masa mafarkin da ya yi. Sai suka hallara a gaban sarki.


Duniya ta girgiza, tana makyarkyata saboda azaba, Gama nufin Ubangiji na gāba da Babila ya tabbata, Nufinsa na mai da ƙasar Babila kufai, inda ba kowa.


Ita kuwa ta ce musu, “Kada ku kira ni Na'omi, wato mai farin ciki, sai dai Mara, wato mai baƙin ciki, gama Mai Iko Dukka ya wahalshe ni ƙwarai.


sai kuma Malon da Kiliyon suka rasu, Na'omi kuwa ta rasa mijinta da kuma 'ya'yanta maza biyu.


Sa'ad da suke cikin halin ƙaƙa naka yi, za a fyaɗa 'ya'yansu ƙasa, su mutu. Za a washe gidajensu, a yi wa matansu faɗe.”


Farat ɗaya sai ga su sun zo! Suna tafe a kan dawakai biyu biyu. Sai mai tsaro ya ba da labari cewa, “Babila ta fāɗi! Dukan gumakan da suke yi wa sujada an ragargaza su har ƙasa.”


Duk da haka bala'i zai auko miki, Ba ɗaya daga cikin sihirinki da zai tsai da shi ba, Lalacewa za ta auko a kanki farat ɗaya, Lalacewar da ba ki taɓa ko mafarkinta ba!


Ita wadda ta haifi 'ya'ya bakwai ta yi yaushi ta suma, Ranarta ta faɗi tun lokaci bai yi ba, An kunyatar da ita, an wulakantar da ita. Waɗanda suka ragu daga cikinsu Zan bashe su ga takobi gaban abokan gābansu. Ni Ubangiji na faɗa.”


A wannan dare kuwa aka kashe Belshazzar Sarkin Kaldiyawa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ