Ishaya 47:8 - Littafi Mai Tsarki8 “Ki kasa kunne, ke mai ƙaunar nishaɗi, Ke da kike tsammani kina zaune lami lafiya. Kin ɗauka kina da girma kamar Allah, Har kina ganin ba wani kamarki. Kina tsammani ba za ki taɓa zama gwauruwa ba, Ko ki sha hasarar 'ya'yanki. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20208 “To, yanzu fa, ki kasa kunne, ke mai ƙaunar nishaɗi, mai zama da rai kwance kina kuma ce wa kanki, ‘Ni ce, kuma babu wani in ban da ni. Ba zan taɓa zama gwauruwa ko in sha wahalar rashin ’ya’ya ba.’ အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Maimakon haka, sai ka nuna wa Ubangiji girmankai, har ka sa aka kawo maka, kai da fādawanka, da matanka, da ƙwaraƙwaranka, tasoshin Haikalin Ubangiji, kuka sha ruwan inabi a cikinsu. Kuka yabi gumakan zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba su ji, ba su gani, ba su da ganewar kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.