Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 45:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Zan ba ka dukiya daga cikin duhu, a asirtattun wurare, Sa'an nan za ka sani ni ne Ubangiji, Allah na Isra'ila kuma, shi ne ya zaɓe ka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Zan ba ka dukiyar duhu, arzikin da aka ajiye a asirtattun wurare, saboda ka san cewa ni ne Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya kira ka da suna.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 45:3
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ni ne na yi magana, na kuwa kira shi, Na yi masa jagora na kuwa ba shi nasara.


Ya Isra'ila, Ubangiji wanda ya halicce ku ya ce, “Kada ku ji tsoro, na fanshe ku. Na kira ku da sunanku, ku nawa ne.


Ga shelar, “In ji Sairus Sarkin Farisa, Ubangiji, Allah na samaniya ya ba ni sarautar dukan duniya, ya kuma umarce ni in gina masa Haikali a Urushalima, ta ƙasar Yahuza.


Musa ya ce wa Ubangiji, “Ga shi, ka faɗa mini cewa, ‘Ka fito da mutanen nan,’ amma ba ka sanar da ni wanda zai tafi tare da ni ba. Ga shi kuma, ka ce, ‘Na san ka, na san sunanka, ka kuma sami tagomashi a gare ni.’


Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Zan yi yadda ka ce, gama ka sami tagomashi a wurina, na san ka, na kuma san sunanka.”


Akwai takobi a kan mahayan dawakanta, da a kan karusanta, Da a kan sojojin da ta yi ijara da su Don su zama kamar mata, Akwai takobi a kan dukan dukiyarta domin a washe ta.


Ko da Babila za ta hau samaniya, Ta gina kagara mai ƙarfi a can, Duk da haka zan aiki masu hallakarwa a kanta, Ni Ubangiji na faɗa.”


Ku kasa kunne gare ni, ku al'ummai manisanta, Ku mutanen da suke zaune a can nesa! Ubangiji ya zaɓe ni, tun kafin a haife ni, Ya kuwa sa ni in zama bawansa.


Amma waɗansu mutum goma daga cikinsu suka ce wa Isma'ila, “Kada ka kashe mu, gama muna da rumbunan alkama, da na sha'ir, da kuma man zaitun da zuma a ɓoye a cikin gonaki.” Sai ya bar su, bai kashe su tare da abokansu ba.


Ku faɗa mana abin da gaba ta ƙunsa. Sa'an nan za mu sani, ku alloli ne! Ku aikata wani abu mai kyau, ko ku kawo wani bala'i, Ku cika mu da jin tsoro da fargaba!


Ku zo, ku fāɗa mata daga kowane sashi. Ku buɗe rumbunanta, Ku tsittsiba ta kamar tsibin hatsi, Ku hallakar da ita ɗungum, Kada wani abu nata ya ragu.


Ƙarshenki ya zo, Ke mai zama kusa da ruwa mai yawa, Mai yawan dukiya. Ajalinki ya auka.


Saboda haka, ya Ubangiji, Allah na Isra'ila, ka tabbatar da maganarka wadda ka yi wa bawanka Dawuda.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ