Na yi fushi da su saboda muguntar kwaɗayinsu, don haka na buge su. Na ɓoye fuskata, na yi fushi. Amma sun yi taurinkai, sun yi ta komawa da baya, sun bi son zuciyarsu.
Sa'an nan suka ce wa macen, “Yanzu kam, mun ba da gaskiya, ba don abin da kika faɗa kawai ba, domin mu ma mun ji da kanmu, mun kuma tabbata lalle wannan shi ne Mai Ceton duniya.”
Al'ummai da sarakuna za su lura da ke Kamar yadda uwa take lura da ɗanta. Za ki sani, ni Ubangiji, na cece ki, Allah Mai Iko Dukka na Isra'ila ya fanshe ki.
“Sa'ad da kuke ɗaga hannuwanku wajen yin addu'a, ba zan dube ku ba. Kome yawan addu'ar da kuka yi, ba zan kasa kunne ba domin zunubi ya ɓata hannuwanku.
Za su zama alamu na kasancewar Ubangiji Mai Runduna a Masar. Sa'ad da aka zalunci mutanen da suke can, za su yi kira ga Ubangiji su nemi taimako, zai aika musu wanda zai kuɓutar da su.