Ishaya 44:9 - Littafi Mai Tsarki9 Dukan waɗanda suke ƙera gumaka mutanen banza ne, gumakan da suke sa wa kuɗi da tsada kuma aikin banza ne. Waɗanda suke yi wa gumaka sujada kuwa makafi ne su, jahilai, za su sha kunya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20209 Duk masu yin gumaka ba kome ba ne, da kuma abubuwan da suke ɗauka da daraja banza ne. Waɗanda za su yi magana a madadinsu makafi ne; jahilai ne, marasa kunya. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Maimakon haka, sai ka nuna wa Ubangiji girmankai, har ka sa aka kawo maka, kai da fādawanka, da matanka, da ƙwaraƙwaranka, tasoshin Haikalin Ubangiji, kuka sha ruwan inabi a cikinsu. Kuka yabi gumakan zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba su ji, ba su gani, ba su da ganewar kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.