Ubangiji ya ce, “Kada ka ji tsoro, ya barana Yakubu, Kada kuma ka yi fargaba, ya Isra'ila, Gama zan cece ka daga ƙasa mai nisa, Zan kuma ceci zuriyarka daga ƙasar bautarsu. Yakubu zai komo, ya yi zamansa rai a kwance, Ba kuwa za a tsoratar da shi ba.
Zaki ya hauro daga cikin ruƙuƙinsa, Mai hallaka al'ummai ya kama hanya, Ya fito daga wurin zamansa don ya mai da ƙasarku kufai, Ya lalatar da biranenku, su zama kango, ba kowa.
“Ya mutanen Urushalima! Ya mutanen Urushalima! Masu kisan annabawa, masu jifan waɗanda aka aiko gare ku! Sau nawa ne ina so in tattaro ku kamar yadda kaza take tattara 'yan tsakinta a cikin fikafikanta, amma kun ƙi!
“Ku mutanena, ku kasa kunne yanzu, ku zo gare ni, Ku zo gare ni, za ku kuwa sami rai! Zan yi tabbataccen alkawari da ku, Zan sa muku albarkun da na alkawarta wa Dawuda.