Ishaya 43:23 - Littafi Mai Tsarki23 Ba ku kawo mini hadayun ƙonawa na tumaki ba, Ba ni kuke girmamawa da hadayunku ba. Ban nawaita muku da neman hadayu ba, Ko in gajiyar da ku da roƙon turare. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202023 Ba ku kawo mini tumaki don hadaya ta ƙonewa ba, balle ku girmama ni da hadayunku. Ban nawaita muku da hadaya ta gari ba balle in gajiyar da ku da bukatar turare. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Mutane suna yin abin da suka ga dama. Suna kashe bijimi domin hadaya, ko su yi hadaya da mutum. Sukan yi hadaya da ɗan rago, ko kuwa su karye wuyan kare. Sukan miƙa hadaya ta hatsi, ko kuwa su miƙa jinin alade. Suna miƙa turare, ko kuwa su yi addu'a ga gumaka. Suna jin daɗin al'amuran banƙyama a lokacin yin sujada.