Ishaya 42:22 - Littafi Mai Tsarki22 Amma yanzu an washe mutanensa, Aka kukkulle su a kurkuku, Aka ɓoye su a rami. Aka yi musu fashi, aka washe su, Ba wanda ya zo domin ya kuɓutar da su. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202022 Amma ga mutanen da aka washe aka kuma kwashe ganima, an yi wa dukansu tarko a cikin rammuka ko kuma an ɓoye su cikin kurkuku. Sun zama ganima, babu wani da zai kuɓutar da su; an mai da su ganima, ba wanda zai ce, “Mayar da su.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Daga waccan ƙasar wakilai sukan gangaro daga Kogin Nilu a cikin jiragen ruwa da aka yi da iwa. Ku koma gida, ku manzanni masu gaggawa! Ku kai saƙo ƙasarku, can a mafarin Kogin Nilu, zuwa ga al'ummarku mai ƙarfi mai iko, zuwa ga dogayen mutanenku masu sulɓin jiki, waɗanda ake jin tsoronsu ko'ina a duniya.
Ni kaina na iza Sairus ya yi wani abu, Don ya cika nufina ya daidaita al'amura. Zan miƙar da kowace hanyar da zai yi tafiya a kai. Zai sāke gina birnina, wato Urushalima, Ya kuma 'yantar da mutanena da suke bautar talala. Ba wanda ya yi ijara da shi, ko ya ba shi rashawa don ya yi wannan.” Ubangiji Mai Runduna ne ya faɗi wannan.