Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ishaya 42:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Akwai sauran wanda ya fi bawana makanta, Ko wanda ya fi manzona kurunta, wato wanda na aiko?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Wane ne makaho in ba bawana ba, da kuma kurma in ba ɗan aikan da na aika ba? Wane ne makaho kamar wanda ya miƙa kai gare ni, makaho kamar bawan Ubangiji?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ishaya 42:19
26 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Su ne marasa ba da gaskiya, waɗanda sarkin zamanin nan ya makantar da hankalinsu, don kada hasken bisharar ɗaukakar Almasihu, shi da yake surar Allah, ya haskaka su.


“Ɗan mutum, kana zaune a tsakiyar gidan 'yan tawaye da suke da idanun gani, amma ba sa gani, suna da kunnuwa na ji, amma ba sa ji, gama su 'yan tawaye ne.


‘Ku ji wannan, ya ku wawaye, marasa hankali, Kuna da idanu, amma ba ku gani, Kuna da kunnuwa, amma ba ku ji.’ ”


'Yan'uwa, ga wata asirtacciyar gaskiya da nake so ku sani, domin kada ku zaci ku masu hikima ne, taurarewar nan–wadda ba mai tabbata ba ce–ta sami Isra'ilawa ne, har adadin al'ummai masu ɗungumawa zuwa ga Allah ya cika.


“Ya makantar da su, ya kuma taurarar da zuciya tasu, Kada su gani da idanunsu, su kuma gane a zuci, Har su juyo gare ni in warkar da su.”


Yesu ya ce musu, “Ai, da makafi ne ku, da ba ku da zunubi. Amma da yake kun ce kuna gani, to, zunubinku ya tabbata.


Yesu ya ce, “Na shigo duniyan nan ne don rarrabewa, domin waɗanda ba sa gani su gani, waɗanda suke gani kuma su makance.”


Ubangiji ya ce, “Mutanena wawaye ne, Ba su san ni ba, Yara ne dakikai, Ba su da ganewa. Suna gwanance da aikin mugunta, Amma ba su san yadda za su yi nagarta ba.”


Matsaransa makafi ne, dukansu marasa ilimi ne. Dukansu kamar karnuka ne bebaye, ba su iya haushi ba, suna kwance suna ta mafarki, suna jin daɗin rurumi!


Amma sa'ad da bawana ya yi annabci, Sa'ad da na aika da manzona domin ya bayyana shirye-shiryena, Na sa waɗannan shirye-shirye da annabce-annabce su cika. Ina faɗa wa Urushalima, cewa mutane za su sāke zauna a can, Za a kuma sāke gina biranen Yahuza. Waɗannan birane za su daina zama kufai.


“Amma kai, Isra'ila bawana, Kai ne jama'ar da na zaɓa, Zuriyar Ibrahim, abokina,


Kai kake ba da cikakkiyar salama, ya Ubangiji, Ga waɗanda suke riƙe da manufarsu da ƙarfi, Waɗanda suke dogara gare ka.


Saboda haka sai ya ce mini in tafi in faɗa wa jama'a wannan jawabi cewa, “Kome yawan kasa kunne da za ku yi, ba za ku fahimta ba. Kome yawan dubawar da za ku yi, ba za ku san abin da yake faruwa ba.”


Shi ya sa nake musu magana da misalai, don ko sun duba ba sa gani, ko sun saurara ba sa ji, ba sa kuma fahimta.


Amma idan maƙiyan jama'ata suna so in cece su, sai su yi sulhu da ni, i, bari su yi sulhu da ni.”


A wannan rana, kurame za su ji sa'ad da aka karanta littafi da murya, makafi kuwa waɗanda suke zaune cikin duhu za su buɗe idanunsu su gani.


Allah ya ce, “Kirawo mutanena a ɗakin shari'a. Suna da idanu, amma makafi ne, Suna da kunnuwa, amma kurame ne!


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ