Ku yi siffofin marurai da na ɓeraye waɗanda suka lalatar da ƙasar, ku ba da girma ga Allah na Isra'ila, watakila zai ɗauke hukuncinsa a kanku, da allolinku, da ƙasarku.
A wannan rana jama'a za su raira waƙa, su ce, “Ku yi wa Ubangiji godiya! Ku nemi taimako a gare shi! Ku faɗa wa dukan sauran al'umma abin da ya aikata! Ku faɗa musu irin girman da yake da shi!